Birtaniya: Jam'iyyar Conservative Ba Ta Samu Rinjayen Da Take Bukata Ba
(last modified Fri, 09 Jun 2017 06:26:07 GMT )
Jun 09, 2017 06:26 UTC
  • Birtaniya: Jam'iyyar Conservative Ba Ta Samu Rinjayen Da Take Bukata Ba

Rahotanni daga Burtaniya na nuni da cewa sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka gudanar jiya, jam'iyyar masu ra'ayin rikau mai mulki ba ta samu rinjayen da take bukata ba.

Jam'iyyar ta conservative dai wadda ya ta samu kujeru 326 daga cikin kujeru 650 na majalisar ya zuwa yanzu da ake gab da kammala kidaya kuri'un baki daya, hakan na nuni da cewa ba za ta iya kafa gwamnati ita kadai ba.

An dai gudanar da zaben ne na ba zata bayan da Fira ministar Birtaniya Theresa May ta bukaci hakan a cikin watan Afirilun da ya gabata, bisa zaton cewa za ta samu gagarumin rinjayen da zai bata damar kafa gwamnati ita kadai.

Yanzu dai ana sa ran jam'iyyar ta Conservative za ta yi hadaka da wata jam'iyyar ne ne domin kafa gwamnati, yayin da shi kuma shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn wanda jam'iyyarsa take a matsai na biyu, ya bayyana hakan a matsayin babban ci gaba ta fuskar dimukradiyya.