An Fara Zaben 'Yan Majalisa A Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21226-an_fara_zaben_'yan_majalisa_a_faransa
Al'ummar Kasar Faransa na kada kuru'unsu domin zaben sabbin wakilan majalisar kasar karkashin sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 11, 2017 07:43 UTC
  • An Fara Zaben 'Yan Majalisa A Faransa

Al'ummar Kasar Faransa na kada kuru'unsu domin zaben sabbin wakilan majalisar kasar karkashin sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron

Da misalain karfe 8 na Safiyar yau Lahadi ne, Al'ummar kasar Faransa suka fara kada kuri'insu domin zaben sabin wakilan Majalisar kasar da adadinsu ya kai 577, wata guda bayan zaben Sabon Shugaba Emmanuel Macron.

Masu sharhi na ganin cewa   jam'iar Shugaba Emmanuel Macron za ta samu nasara a zaben na yau.

Nasarar da Shugaba Emmanuel Macron ya samu a watan jiya ya haifarda  sabon salo a siyasar Faransa kuma jam'iyar sa na fatan ganin sun sami rinjayen wakilai a majalisa don su sami aiwatar da manufofinsu ba tare da jibin goshi ba.