An Kame Irakawa Bakin Haure 199 A Kasar Amurka
(last modified Thu, 15 Jun 2017 11:09:40 GMT )
Jun 15, 2017 11:09 UTC
  • An Kame Irakawa Bakin Haure 199 A Kasar Amurka

An Kame Irakawa 199 dake zaune a kasar Amurka ba kan ka'ida ba

Kamfanin dillancin labaran Saumaria na kasar Iraki ya nakalto Jami'an kasar Amurka na cewa Irakawa 199 dake zaune a kasar ba kan ka'ida ba mafi yawa a garin Detroit aka kame cikin makuni uku na baya bayan nan, kuma tuni aka fara mayar da su kasar su bayan amincewar Gwamnatin ta Iraki.

A cewar Kakakin Ma'aikatar tsaron cikin gidan Amurka Gillian Christensen Irakawa 114 ne aka kama a garin Detroit cikin wannan Mako, yayin da a makonni biyun da suka gabata aka kame 85.

Kakakin Ma'aikatar tsaron cikin gidan na Amurka ya kara da cewa a cikin watan Afirilun na wannan shekara da muke ciki ta 2017, an samar da kudirin fitar da Irakawa kimanin dubu daya da dari biyar daga cikin kasar ta Amurka kuma daga ranar 12 ga watan Maris da ya gabata zuwa yanzu Irakiyawa 12 ne kacal suka koma kasar su.