Majalisar Dattawan Amurka Ta Amunce Kakabawa Iran Sabon Takunkumi
(last modified Fri, 16 Jun 2017 04:38:00 GMT )
Jun 16, 2017 04:38 UTC
  • Majalisar Dattawan Amurka Ta Amunce Kakabawa Iran Sabon Takunkumi

Majalisar dattawan kasar Amurka, ta zartas da wani daftarin doka dake da nufin sake kakabawa kasar Iran takunkumi.

Ana sa ran nan gaba kadan, za a gabatar da daftarin ga majalisar wakilan kasar, domin ta ci gaba da nazarinsa.

Bisa wannan daftari dai, kasar Amurka za ta sanyawa dukkanin masu hannu cikin shirin bunkasa makamai masu linzami na kasar Iran takunkumi, da kuma wadanda suka taba yin cinikayya da wadannan mutane.

Haka kuma a karon farko daftarin ya bukaci Amurka ta sanyawa dakarun kare juyin juya halin Islama na Iran cewa da (IRGC) takunkumi bisa zargin cewar suna da alaka da 'yan ta'adda.

Ko baya ga hakan daftarin ya tanadi karfafa matakan da za a dauka na safarar makamai da kayan soji zuwa Iran.

Ko bayan ga Iran, daftarin ya tanaji kakabawa wasu jami'an kasar Rasha takunkumi, bisa zargin keta hakkin bil Adama, da karbar rashawa, da samar da makamai ga gwamnatin kasar Syria, da ba da taimako ga Rasha a fannin yin kutse ta intanet a harkokin zaben Amurka.