Harin Ta'addanci Ya Halaka Mutum Guda A Colambia
Jun 18, 2017 05:44 UTC
Wani Bam ya fashe a Bogotá fadar milkin kasar Colambia, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da jikkatar wasu 11 na daban
kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Magajin garin Bogotá na cewa tashin Bam din ya faru ne a wata cibiyar kasuwanci dake cikin birnin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutum guda tare da raunana wasu 11 na daban.
Faifan videon farko da kafafen yada labaran kasar suka nuna ya nuna mutanan da suka jikkata a inda lamarin da ya auku.kamar yadda rahoton ke cewa Bam din ya tashi ne a hawa na biyu na ginin cibiyar kasuwancin Centro Andino.
Ya zuwa yanzu baba wata kungiya ko wani gungu da ya dauki alhakin kai harin.
Tags