Musulmi Birtaniya Sun Bukaci Mahukuntan Kasar Da Su Kare Wuraren Ibada
Majlaisar musulmin kasar Birtaniya ta bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakan kare wuraren ibada da suka hada da masallatai da kuma cibiyoyin musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran AP ya bayar da rahoton cewa, Harun Khan shugaban majalisar musulmin kasar Birtaniya, ya kirayi mahukuntan kasar da cewa, lokaci ya yi da za su daukin nauyin tabbatar da tsaro a wuraren ibadar musulmi, maimakon barin su a cikin halin rashin tabbas ta fuskar tsaro.
Ya ce harin da aka kai ma musulmi yau da sassafe ba shi ne irinsa na farko ba, hakan na faruwa sau da dama a sassa daban-daban na kasar, inda ko mako guda ba ayi ba da cinna wuta akan wani dogon bene da musulmi ne mafi yawan mutanen da suke a cikinsa, a yau kuma an kai musu hari har a wurin ibada a cikin birnin an London.
Ya kara da cewa wadannan abubuwa suna faruwa ne sakamakon karuwar kyamar musulmia tsakanin wasu 'yan kasar ta Birtaniya, alhali musulmin da suke a kasar su ma 'yan kasa ne da suke da dukaknin hakkoki kamar kowane dan kasa, kuma a bisa doka dole ne a kare ma musulmi na hakkokin, tare da basu kariya da kuma tsaron lafiyarsu da kaddarorinsu da mutuncinsu.