Ana Tuhumar Shugaban Brazil Da Karabar Cin Hanci Da Rashawa
(last modified Tue, 27 Jun 2017 05:18:59 GMT )
Jun 27, 2017 05:18 UTC
  • Ana Tuhumar Shugaban Brazil Da Karabar Cin Hanci Da Rashawa

Babban mai shigar da kara na kasar Brazil Rodrigo Janot ya bukaci kotun kolin kasar da ta gabatar da tuhuma a hukumance a kan shugaban kasar Michel Temer bisa zarginsa da laifin karbar cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, babban mai shigar da kara na kasar Brazil ya tuhumi shugaban kasar da yin amfani da matsayinsa domin karbar kudade na cin hanci daga shugaban wani kamfani a kasar wanda shi ma ake zargin sa da manyan laifuka cin hanci.

Kafin kotun kolin ta kasar Brazil ta gurfanar shugaban kasar, sai kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar kasar sun amince a hakan, za a iya dakatar da ayyukan shugaban kasar har na tsawon watanni 6, wanda kuma hakan kaa iya kaiwa ga tsige shi daga kan mukaminsa.

Baya ga zargin cin hanci da rashawa, akwai wasu zarge-zarge a kan shugaban na Brazil, da suka hada da kawo tarnaki ga ayyukan shari'a a kasar, da kuma kafa kungiyoyin 'yan daba da ke cutar da al'umma.