Bincike : Saudiyya Ta Kashe Milyoyin Daloli Don Yada Tsatsauran Ra'ayin Addini
Wani rahoto da wata kungiyar kwararru ta Henry Jackson Society ta fitar ya zargi Saudiyya da yada tsatsaran ra'ayin addinin islama a turai.
Rahoton da kungiyar ta Biritaniya ta fitar yau Laraba ya ce daga shekara 1960 masarautar Saudiyya ta kashe miliyoyin daloli wajen yada akidar wahabiyanci a cikin al'ummar musulmi na kasahen Turai.
Hakazalika rahoton ya kuma zayyano kasashen da suka hada da Hadaddiyar daular Larabawa, Kowait, Qatar da kuma Iran da wannan zargin, saidai ya ce na Saudiyya fa muni idan aka kwatantan da wandanan kasashen.
A cewar rahoton ana amfani da taimakon ne wajen gina masallatai da makarantu inda malamai ke koyarda tsatsaran ra'ayyin addinin na islama dake haifar da ayyukan ta'addanci.
kana kuma wasu mayan malaman an horada dasu kan wannan akidar a Saudiyya.
Rahoton wanda kungiyar da ke tallata manufofin kasashen waje ta hanyar yada dimokradiyya, da bin doka da kuma tattalin arziki ya bukaci gwamnatin Biritaniya data kaddamar da wani bincike na jama'a da kuma kara cilasta bada haske kan safara kudade tsakanin kasar da kasashen ketare musamen na Saudiyyar.