Iraki : Ana Ci Gaba Da Jinjinawa Dakarun Da Suka Kwato Mosul
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22058-iraki_ana_ci_gaba_da_jinjinawa_dakarun_da_suka_kwato_mosul
Duniya na ci gaba da jinjinawa sojojin Iraki da dukkan dakarun da suka taimaka wajen kwato birnin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 10, 2017 06:17 UTC
  • Iraki : Ana Ci Gaba Da Jinjinawa Dakarun Da Suka Kwato Mosul

Duniya na ci gaba da jinjinawa sojojin Iraki da dukkan dakarun da suka taimaka wajen kwato birnin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh.

Sakon baya bayan nan shi ne na shugaba Emmanuel Macron na faransa wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, Faransa tana jinjinawa sojojin Iraki da dukkan dakarun, ciki har da na kasarsa da suka taimakwa wajen kwato tsohon birnin na Mosul.

A jiya Lahadi ne firaministan Iraki ya ziyarci Mosul inda ya sanar da murkushe 'yan ta'addan daga birnin, bayan kwashe kusan watanni tara na fafatawa da kungiyar.

'Yantar da birnin Mosul dake zamen babban sansani na kungiyar IS a Iraki tun cikin shekara 2014, ita ce kawo yanzu wata babbar nasara da aka samu kan 'yan ta'addan na IS.