Amurka : Trump, Ya Tsawaita Lokacin Cirewa Sudan Takunkumi
(last modified Wed, 12 Jul 2017 05:49:29 GMT )
Jul 12, 2017 05:49 UTC
  • Amurka : Trump, Ya Tsawaita Lokacin Cirewa Sudan Takunkumi

Shugaba Donald Trump na Amurka ya tsawaita da watanni uku lokacin tsammanin cirewa kasar Sudan takunkumin tattalin arziki na tsawan shekaru 20 da ya ragargaza tattalin arzikin kasar.

Tsohon shugaban Amurkar ce Barack Obama ne a kwanakin karshen wa'addin mulkinsa ya dau matakin tsammanin dagewa Sudan wasu jerin takunkumi a cikin watanni shida, kafin aiwatar da matakin kwata-kwata. 

A yau Laraba ne 12 ga wata matakin ke kawo karshe, saidai shugaba Trump ya tsawaita shi har zuwa 12 ga watan Oktoba na wannan shekara, kamar yadda wata sanarwa da kakakin ma'aikatar diplomatsiyya Amurka Heather Nauert ya fitar.

Sanarwar dai ta Amurka za ta iya dage duk jerin takunkuman muddun dai gwamnatin Khartoum ta nuna da gaske ta ke musammen yakin da take a yankunan dake fama da rikici, samar da hanyoyin isar da kayan agaji  da kuma karkafa hadin gwiwarta da Amurka wajen shawo rigingimu a yankin da kuma barazana ta'addanci.