Gwamnatin Jamus Ta Yi Kakkausar Suka Kan Dabi'ar Fataucin Bil-Adama
Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus ya yi kakkausar suka kan mummunar dabi'ar nan ta fataucin bil-Adama musamman ganin yadda bakin haure suke rasa rayukansu a tekun Mediterrenea.
Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus Thomas de Maiziere ya bayyana cewa: Mummunar dabi'ar nan ta fataucin bil-Adama tana ci gaba da lashe rayukan jama'a tare da wurga wasu cikin mawuyacin hali musamman ganin yadda bakin haure suke ci gaba da halaka a tekun mediterrenea.
Thomas de Maiziere ya kara da cewa: Sana'ar fataucin bil-Adama tana daga cikin manyan laifukan cin zarfin dan Adam a wannan lokaci musamman ganin yadda wannan mummunar sana'ar take ci gaba da janyo hasarar rayukan mutane tare da wurga su cikin halin kaka-ni ka yi, kamar yadda masu sana'ar suke rayuwa da kudaden bakin haure da suka cikin mummunan kangi a fagen rayuwarsu.
A duk shekara dai dubban bakin haure ne suke mutuwa a tekun Mediterrenea a kokarin da suke yi na neman shiga cikin kasashen yammacin Turai ta hanyar teku, inda a cikin watanni shidan farkon wannan shekara ta 2017 fiye da bakin haure 2,000 ne suka rasa rayukansu a cikin tekun.