Jamus : An Cafke Ton 3,8 Na Hodar Iblis
Jul 20, 2017 19:00 UTC
Jami'an Kostom a Jamus sun yi wani wawan kamu na kusan ton hudu na hodar Iblis a tashar ruwan Hambourg.
An dai cafke hodar ne a lokacin da ake kokarin shigo da ita cikin kasar daga kudancin Amurka.
An kiyasta kudinta zasu kai Milyan 800 na kudin Yuro.
Wannan dai shi kamu mafi girmna a aka taba gani a wannan kasar ta Jamus.
A cen baya dai jami'an Kostom kan yin kame na Hodar Iblis saidai bata fiye ta kai kilo 50 zuwa 150 ba.
Amman a baya bayan nan lamarin ya yi kamari inda jami'an kan kai ga cafke hodar Iblis data kai ton guda zuwa guda da rabi.
Tags