Aug 01, 2017 17:13 UTC
  • Kasashen Musulmi Sunyi Tir Da Halin Tsokana Na H.K. Isra'ila

Wakilan kasashen musulmi 57 na kungiyar OIC da suka taru yau a birnin Satambul na Turkiyya sunyi tir da abunda suka kira tsokana na yahudawan mamaya na Isra'ila a masallacin Al'Aqsa dake birnin Qudus.

Taron na ministocin harkokin wajen kungiyar na a matsayin maida martani kan Isra'ilar, sakamakon matakan data dauka a kwanakin baya na hana Palasdinawa da kristoci gudanar da ibada da kuma matakan wuce gona da iri da take dauka na kashin kanta a masallacin.

A yayin bude taron, ministan harkokin wajen Palastine Riyad al-Malki ya zargi firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da yunkurin canza yarjejeniyar shekaru da shekaru da aka cimma wacce ta baiwa muslmi damar yin sallah a harabar masallacin a ko wanne lokaci, yayin da su kuwa yahudawa suke da damar ziyartar wurin a wasu lokaci aman ba tare da gudanar da shagulgula ba.

Shi kuwa a nasa bangare ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, wanda kasarsa ke rike da shugabancin kungiyar ta OIC kira ya yi ga kasashen musulmi da su goyi bayan Palasdinu a zahiri ba wai babatu ba, tare da kiran a tashi tsaye domin kare masallacin na Al'Aqsa da kuma Palastine.

Kalamen na sa dai na zuwa kwanaki kadan bayan shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga dukkan musulmi dasu ziyarci birnin Qudus.

Tags