Kasar China Ta Yi Alkawarin Taimakawa Kasar Gambiya
Ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi ya bayyana cewar kasar Chinan ta yi alkawarin taimakawa kasar Gambiya a bangaren ayyukan gona, yawon shakatawa da sauran fannoni.
Ministan harkokin wajen kasar China ya bayyana hakan ne a lokacin da yake maraba da takwararsa ta kasar Gambiyan Ousainou Darboe a ziyarar da ta kai kasar Chinan inda ya ce kasar China tana shirye ta karfafa alakarta da kasar Gambiya a bangaren ayyukan gona, yawon shakatawa da sauran fannoni.
Wannan alkawarin dai ya zo ne bayan da kasar Gambiyan ta katse alakarta da yankin Taiwan wanda kasar Chinan take ganin a matsayin wani bangare na kasarta. Tun da jimawa dai sabuwar gwamnatin kasar Gambiyan ta sanar da alakarta ta karfafa alaka da kasar China da kuma kawo karshen alakar diplomasiyya da Taiwan din.
Kasar China tana gasa da kasar Faransa wajen samun damar sake gina tashar bakin ruwa na Banjul wanda ake ganin zai taimaka wa kasar Gambiya a fagen tattalin arziki.