Amurka Za Ta Sayarwa Najeriya Jiragen Yaki Na Zamani
Gwamnatin Amurka ta amince sayarwa da Najeriya jiragen saman yakin zamani har na dala Miliyan 600, duk kuwa da zargin keta hakkin bil Adama da ake yiwa Najeriyar.
A ranar Alhamis ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta ce ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da cinikin, ta kuma mika batun ga ‘yan Majalisar Dokokin Amurkar, wadanda ke da kwanaki 30 su amince da cinikin.
Yarjejeniyar ta kunshi saidawa Nigeria jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12, wadanda ake amfani da su wajen kai kananan hare-hare.
Ma’aikatar tsaron Amurka ta ce jiragen zasu taimakawa sojojin Najeriya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram, zasu kuma taimaka wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi da makamai da kuma safarar mutane.
Tsohon shugaba Barack Obama na Amurka ce ya dakatar da yarjejeniyar cinikin jiragen, biyo bayan harin da wani jirgin saman yakin Najeirya ya kai kan sansanin ‘yan gudun hijira a iyakar Nijeriya da Kamaru.