Fao: Gargadi Akan Fari A Gabacin Nahiyar Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23184-fao_gargadi_akan_fari_a_gabacin_nahiyar_afirka
Hukumar abinci ta duniya( fao) ta yi gargadi akan karuwar mutanen da suke mutuwa saboda fari a gabacin nahiyar Afirka.
(last modified 2018-08-22T07:00:32+00:00 )
Aug 14, 2017 14:24 UTC
  • Fao: Gargadi Akan Fari A Gabacin Nahiyar Afirka

Hukumar abinci ta duniya( fao) ta yi gargadi akan karuwar mutanen da suke mutuwa saboda fari a gabacin nahiyar Afirka.

Rahoton na hukumar abinci ta Fa'o wanda Rediyon Faransa na kasa da kasa ya ambato  ya maida hankali akan kasa Habasha a matsayin inda aka fi samun asarar rayukan.

Rahoton ya ambaci bayyanar yanayin Elnino wanda ya ke samun asali daga raguwar saukar ruwan sama, da sakamakonsa shi ne karancin abinda ake nomawa.

Wani sashe na rahoton ya ce a halin da ake ciki da akwai mutane kusan miliyan takwas da rabi a cikin kasar ta Habasha da su ke cikin yunwa, miliyan uku daga cikinsu suna matsananci hali.

Hukumar ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo dauki domin ceto da rayukan mutane.