Spain: An Kashe Mutumin Da Ya Kai Harin Barcelona
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23406-spain_an_kashe_mutumin_da_ya_kai_harin_barcelona
Jami'an tsaron kasar Spain sun ce sun samu nasarar kashe Yunusu Abu Ya'akub dan kasar Morocco wanda ya kai hari a birnin Barcelona a ranar Alhamis da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T11:30:34+00:00 )
Aug 21, 2017 19:11 UTC
  • Spain: An Kashe Mutumin Da Ya Kai Harin Barcelona

Jami'an tsaron kasar Spain sun ce sun samu nasarar kashe Yunusu Abu Ya'akub dan kasar Morocco wanda ya kai hari a birnin Barcelona a ranar Alhamis da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Majiyoyin tsaron sun ce an kashe Yunus Abu Ya'akub ne a yau a wani wuri mai tazarara kilo mita 60 a wajen birnin Barcelona, kuma an samu jigidar nakiyoyi a jikinsa.

Tun bayan harin ranar Alhamis da ta gabata da aka kai a cikin birnin Barcelona, musulmi a birnin suke cikin tsoro.

Raja Miyah shi ne limamin wani masallaci da ke tsakiyar birnin na Barcelona ya bayyana cewa, tun bayan kai harin adadin musulmi masu zuwa salla a masallacin ya ragu matuka, domin kuwa suna jin tsoron cewa a kowane lokaci za a iya kawo ma masallacin hari da sunan daukar fansa a kan musulmi.

A ranar Juma’a da ta gabata, wasu gungun musulmi a birnin na Barcelona sun gudanar da wani gangami, inda suka yi tir da Allah wadai da harin da ‘yan ta’adda suka kai a birnin, tare da nisanta kansu dama addinin msulunci daga wannan mummunan aiki.