Angela Merkel ta kare matsayinta kan 'yan gudun hijira
A yayin gudanar da yakin neman zabe na karshe a zabubbukan 'yan majalisun dokokin jihohi uku da ke a Gabashin Jamus.
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta yi kokarin kare matsayinta kan 'yan gudun hijira da ke ci gaba da shigowa cikin kasar inda ta bayyana cewa
''A wasu lokuta ya zama wajibi a dauki tsauraran matakai ,a yanzu kusan cewa kusan dukkanin kasashen da ke yankin Balkans sun taka rawa akan wannan batun, kuma abubuwa masu tari yawa sun faru a baya ,yana da kyau mu koyi darasi daga kura-kuran da muka tafka a baya ta yadda abubuwa za su kai ga ingantuwa a gaba.''
har ila yau Markel ta kara da cewa mutane sun shigo mana kwatsam suna bukatar taimako idan muna da halin yin hakan sai mutaima kesu.