Addinin Muslunci Na Bunkasa Cikin Sauri A Australia
Wasu rahotanni sun yi nuni da cewa addinin muslunci shi ne addinin da ya fi saurin yaduwa a makarantun jahar New South Wales a kasar Australia.
Jaridar Daily Telegraph da ake bugawa a kasar ta Australia ta bayar da rahoton cewa, sakamakon wani bincike da aka gudanar bisa alkaluman da ma'aikatar ilimi a jahar New South Wales ta bayar ya nuna cewa, adadin dalibai musulmi a makarantun firamare da sakandare yana karuwa fiye da sauran yara mabiya wasu addinai na daban.
Bayanin rahoton wanda jaridar daily telegraph ta buga ya yi ishara da cewa, adadin dalibai musulmi ya kai kimanin kashi 30 cikin dari na dukkanin daliban da ke makarantun firamare da sakandare na jahar.
Haka nan kuma a shekarar bana an samu karuwar dalibai fiye da dubu 2000 musulmi, wanda alkaluman ke nuna cewa karuwar dalibai musulmi a makarantun wannan jaha ya haura na sauran dalibai wadanda ba musulmi ba, inda mabiya addinin hindus ke zuwa a matsayi na biyu bayan musulmi.
A daya bangaren kuma rahoton ya nuna cewa adadin mabiya addinin kirista da suke shiga makarantun bai karu ba idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.