Saudiyya : An Shiga Aikin Hajji Gadan-gadan
Al'hazai da suka taru a Saudiyya domin sauke farali a bana, sun shiga aikin hajji gadan-gadan a yau Laraba.
Maniyyata sama da miliyan biyu ne ake sa ran zasu bar garin Makkah zuwa Mina kafin su wuce zuwa Arfah, mafi muhimmanci ga aikin hajji, wanda shi ne haduwar mutane mafi girma a duniya.
Kafin hakan dai Saudiyya ta ce ta dauki kwararen matakai na tsaro inda aka tanadi dakaru sama da dubu dari domin tunkarar duk wata irin barazana dake iya tasowa.
Ko baya ga batun tsaro hukumomin lafiya na Saudiyya sun ce sun dau suk matakan da suka wajaba domin tunkarar barkewar cutuka ko annoba a lokacin wannan aikin hajjin.
A goda Alhamis ne ake hawan Arafa wanda shi ne kololuwar aikin hajjin.
A shekara 2015 data gabata alhazai kimanin 2,000 ne sukayi shahada a yayin turmususun da aka samu a lokacin jifan shaidan.
Maniyatan Iran na daga cikin mahajatan na bana bayan sun kauracewa aikin hajji a bara saboda turmususun da aka samu.