IAEA: Iran Tana Ci Gaba Da Girmama Yarjejeniyar Nukiliyan 2015
(last modified Thu, 31 Aug 2017 17:55:13 GMT )
Aug 31, 2017 17:55 UTC
  • IAEA: Iran Tana Ci Gaba Da Girmama Yarjejeniyar Nukiliyan 2015

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta sanar da cewa Iran tana ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da ita a shekara ta 2015 don haka babu wata bukatar binciken barikokin sojinta.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce hukumar ta IAEA ta bayyana hakan ne cikin rahoton da ta fitar na rubu'in shekara inda ta ce Iran tana ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliyan da ta cimma da manyan kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran ya jiyo wata majiyar hukuma ta IAEA tana fadin cewa sakamakon ci gaba da girmama yarjejeniyar da Iran take yi don haka babu wata bukata ta gudanar da bincike a sansanonin sojinta.

A kwanakin baya ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tura jakadiyarsa a MDD Nikki Haley zuwa birnin Vienna don ganawa da babban daraktan hukumar ta IAEA da nufin matsa matsa lambar gabatar da bukatar gudanar da bincike a sansanonin sojin Iran a kokarin da gwamnatin Trump din ta ke yi na kara matsin lamba a kan Iran da nufin kara kakaba mata takunkumi lamarin da jami'an Iran din suka yi watsi da shi da cewa babu wani da ya isa ya gudanar da bincike a barikokin sojin kasar don kuwa hakan ma ba ya cikin yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma.