Duniya ta yi Allawadai da harin birnin Ankara
Babban saktaren MDD da Gwamnatocin Amurka da Faransa,cikin wata sanarwa da suka fitar sun yi alawadai da harin ta'addancin da aka kai Ankara babban birnin kasar Turkiya.
A yayin da yake bayyana jimaminsa ga Al'ummar kasar Turkiya Babban saktaren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya yi alawadai da wannan hari na ta'addanci.
Ita ma Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta bayyana harin a matsayin dabbanci sannan kuma ta ce Amurka tana goyon bayan gwamnatin Turkiya a duk wani mataki da za ta dauka wajen yaki da ta'addanci.
A nasa bangare, shugaban kasar Faransa Francois Holland cikin wani jawabi da yayi wa Al'ummar Turkiya ya bayyana Alhinisa garesu jim kadan bayan kai wannan hari, inda ya kara da cewa Faransa za ta yi aiki tare da Turkiya a yaki da ta'addanci.
A jiya Lahadi ne aka kai harin a tashar Bas dake unguwar Kizilay da ke tsakiyar birnin Ankara, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 34 tare da jikkata wasu 129 na daban, 19 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.