MDD Ta Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumai
(last modified Tue, 12 Sep 2017 05:50:42 GMT )
Sep 12, 2017 05:50 UTC
  • MDD Ta Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumai

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da kudirin Amurka na tsananta wasu jerin sabbin takunkumai kan Koriya Ta Arewa bisa gwajin makamin nukiliyarta na baya baya nan.

Kudirin wanda a wannan karon ya samu goyan bayan kasashen China da Rasha aminnan Koriya ta Arewar, ya tanadi matakai masu tsauri na karkato hankalin gwamnatin Pyongyang kan ta tattauna hanyoyin warware shirinta na makaman nukiliya dake zaman babbar barazana ga duniya a cewar MDD.

Sabbin jerin takunkuman sun shafi duk wani harkar man fetur da danginsa da kuma iskar gas, da mayarwa Koriya ta Arewar 'yan kasarta sun kimamin (93,000) a cewar Amurka, da toshe duk wasu kaddarorin shugaba Kim Jong-Un, da kuma haramta odar duk wasu kayan masana'antun tsaka na kasar da kuma aiwatar da bincike da karfin tsiya na duk jiragen ruwa da suka keta shawarwarin MDD.

Wata sanarwa da Koriya ta Kudu ta fitar ta ce ya kamata makofciyyarta Koriya ta Arewa ta gane cewa warware shirinta na Nukiliya shi ne kawai hanyar samar ma kanta zaman lafiya da kuma habaka tattalin arzikinta.

A ranar 3 ga watan nan ne Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani makamin kare dangi, wanda ya tayar da hankalin duniya ba kadan ba, kuma wannan shi ne karo na takwas da ake kakaba mata jerin takunkumai.