Sep 14, 2017 17:05 UTC
  • Majalisar Turai Ta Yi Barazanar Kwacewa Shugabar Myammar Lambar Yabo

Majalisar Turai ta fitar da wata sanarwa a yau Alhamis dake bukatar sojojin Myammar dasu kawo karshen muzgunawar da akewa 'yan kabilar Rohingyas.

A kudirin da kasashen suka amunce da shi a wani taro a birnin Strasbourg, majalisar ta ce ta damu sosai kan cin zarafin bil adama da akewa tsirarun musulmin 'yan Rohingyas a wannan kasa ta Myammar.

Majalisar ta bukaci shugabar gwamnatin ta Myammar, Aung San Suu Kyi, data tsawata tare da yin allawadai da irin cin zarafin da akewa musulmin na Rohingyas, tare da yi mata barazanar kwace lambar yabo ta kare hakkin bil adama da aka bata a shekara 1990.

'Yan majalisar ta Turai sun ce bisa ga yadda shugabar ta Myammar ta yi gum da bakinta kan halin da 'yan Rohingyas ke ciki, tana tunanin tattauna hanyoyin kwace lambar yabon ta ''Sakharov'' da ta baiwa Aung San Suu Kyi kan rawar data taka wajen samar da yancin fadar albarkacin baki a shekara 1990.

A baya bayan nan dai shugabar gwamnatin ta Myammar Aung San Suu Kyi, na shan daga bangarori daban-daban na duniya kan shirun da ta yi kan kisan kiyashin da akewa musulmin 'yan Rophingyas.

Bisa ga hakan dai Aung San Suu Kyi, ta ce ba zata halarci taron koli na MDD,  karo na 72 a birnin New York ba.

Tags