Faransa : Yarjejeniyar Nukiliya Iran, Misali Ne Na Hana Yaduwar Makaman Nukiliya
Kasar Faransa ta bakin ministan harkokin wajenta ta ce yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran, misali ne mai kyawo da zai hana yaduwar makaman nukiliya.
Da yake bayyana hakan a wata hira da manema labarai a birnin New York inda zai halarci babban taron MDD, Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Yves Le Drian ya ce ya na da kyau a ci gaba da aiki da yarjejeniyar da aka cimma da Iran don baiwa sauren bangaroro damar sassautowa kan matsayinsu na mallakar makamin nukiliya.
Mista le Drian ya kara da cewa kasarsa Faransa za ta yi kokarin shayo kan shugaba Donald Trump na Amurka kan mahimmancin wannan batu.
Wadanan kalamen na ma'aikatar harkokin wajen faransa na zuwa ne a lokacin da shugaba Trump ke nuna halin ko in kula akan yarjejeniyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara 2015 akan shirin nukiliyar ta na zamen lafiya da aka jima ana takaddama a kai.
A hannu daya kuma le Drian ya ce kawo yanzu babu wani abu da ya ke nuna masu cewa Iran bata mutunta yarjejeniyar da aka cimma da ita wanda ya kai ga cire mata wasu jerin takunkumai.