An Shelanta Doka Ta Baci A Lardin Kathalonia Na Kasar Espania
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24213-an_shelanta_doka_ta_baci_a_lardin_kathalonia_na_kasar_espania
Gwamnatin Kasar Espania ta shelanta halin doka ta baci a yankin Cathalonia arewa maso gabacin kasar bayan da tashe tashen hankula suka kara yawa a cikin yan kwanakin nan.
(last modified 2018-08-22T11:30:43+00:00 )
Sep 20, 2017 17:10 UTC
  • An Shelanta Doka Ta Baci A Lardin Kathalonia Na Kasar Espania

Gwamnatin Kasar Espania ta shelanta halin doka ta baci a yankin Cathalonia arewa maso gabacin kasar bayan da tashe tashen hankula suka kara yawa a cikin yan kwanakin nan.

Wata jaridar kasar ta Espania Al-mondoo ta bayyana cewa gwamnatin Madrid ta dau wannan matakin ne a yau Laraba a dai dai lokacinda yansandan kasar suka kai sumama a birnin Basalona suka kuma kama kwamitionan tattalin arziki na yankin Josep Maria Jove, kuma makonni biyu kafin a gudanar da zaben raba gardama na bellewar yankin daga kasar Espania.

Har'ila yau wasu jaridun kasar sun bada labarin kama wasu manya manyan jami'an gwamnatin yankin kuma shuwagabannin yan a aware wadanda suke jagorantar shirin zaben raba gardamar.

Gwamnatin kasar Espania da kuma babban kotun kasar duk sun haramta zaben raba gardama na ballewar yankin Cathalonia daga kasar.

Tun shekara ta 2012 ne yankin cathalonia na kasar Espania suke bukatar bellewa daga kasar Espania amma gwamnatin tarayyar kasar ta ki amincewa da hakan.