Zaben Kurdistan Zai Kara Dagula Al'amuran Tsaro_Amurka
Amurka ta sanar da cewa ta ji takaici sosai akan zaben raba gardama ballewar yankin Kurdawan Iraki, tare da cewa hakan zai kara dagula al'amuran tsaro da wahalhalu a yankin.
A wata sanarwa da gwamnmatin Amurka ta fitar, ta ce ba wai hakan yana nufin yanke dadaddiyar alakar dake tsakaninta da al'ummar Kurdawan Iraki ba, aman zaben zai iya kara dagula al'ummar da kuma matsaloli ga yankin Kurdawan dama al'ummarsa.
Haka zalika kuma Amurka ta ce zaben zai iya hadassa zaman doya da man ja tsakanin yankin na Kurdistan da gwamnatin Iraki da kuma kasashe makoftan yankin.
A jiya ne dai Kurdawan Iraki suka kada kuri'ar zaben raba gardama akan neman ballewar yankin domin samar da 'yantaciyyar kasar Kurdawa.
A halin da ake ciki dai gwamnatin Iraki ta sanar da aikewa da dakarun soji a yankunan da ake takkadama akansu.