Rasha Ta Soma Janye Dakarunta Daga Syria
Mar 15, 2016 08:29 UTC
Kasar Rasha ta soma janye dakarun ta daga Syria a wannan Talata bayan da shugaban kasar Vladimir Putin ya sanar da wannnan matakin cikin daren jiya Litinin.
Ministan tsaro kasar ya ce yanzu haka dakarun kasar sun shiga aikin kwashe kayan su daga wannan kasa kuma nan bada jimawa ba zasu fara maido kayan zuwa gida.
Wannnan matakin da shugaban Rasha ya dauka ya zo ma duniya ba-zata, a daidai lokacin bude tattaunawar kawo karshen rikicin Syria da aka shafe shekaru shida ana yi.
Tags