Shugaban Gwamnatin Catalonia: Mun Sami Hakkin Zama Masu 'Yanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24541-shugaban_gwamnatin_catalonia_mun_sami_hakkin_zama_masu_'yanci
Carles Puigdemont wanda shi ne shugaban yankin na Catalonia ya fadi haka ne bayan sanar da sakamakon kuri'ar raba gardama a jiya lahadi.
(last modified 2018-08-22T11:30:46+00:00 )
Oct 02, 2017 07:12 UTC
  • Shugaban Gwamnatin Catalonia: Mun Sami Hakkin Zama Masu 'Yanci

Carles Puigdemont wanda shi ne shugaban yankin na Catalonia ya fadi haka ne bayan sanar da sakamakon kuri'ar raba gardama a jiya lahadi.

Bugu da kari Puigdemont ya kuma ce; Nan da wasu kwanaki gwamnatina za ta aike da sakamakon raba gardamar zuwa ga majalisa domin ta dauki matakan da suka dace akansa.

Sakamakon da aka sanar na kuri'ar raba gardama akan makomar 'yankin na Catalonia, ya nuna cewa kaso 90% sun amince da yankin ya balle daga kasar Spain.

Jami'an tsaron kasar Spain sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu kada kuri'ar a wasu yankuna na Catalonia. Fiye da mutane 844 ne suka jikkata sanadiyyar harin na 'yan sanda.

Tun da fari gwamnatin kasar Spain ta bayyana kada kuri'ar da cewa ya sabawa doka.