Amurka Ta Bukaci Kara Aiko Da Sojoji Dubu Zuwa Kasar Afganistan
(last modified Thu, 05 Oct 2017 16:54:13 GMT )
Oct 05, 2017 16:54 UTC
  • Amurka Ta Bukaci Kara Aiko Da Sojoji Dubu Zuwa Kasar Afganistan

Sabon jakadan Amurka a kungiyar tsaro ta NATO ya bayyana cewa gwamnatin kasarsa ta gabatarwa kungiyar bukatar kara sojojinta dubu guda a kasar Afganisatan

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Kay Bailey Hutchison sabon jakadan Amurka a kungiyar tsaro ta NATO yana fadar haka a yau Alhamis a birnin Brussels na kasar Belgium. Shugaba Donal Trump dai ya yiwa Amurkawa alkawarin zai dawo da sojojin kasar da suke Afganistan gida a lokacin yakin neman zabe, amma a halin yanzu da alamun ya yi watsi da wannan alkawarin.

A halin yanzu dai Amurka tana da sojoji dubu 11 a cikin sojojin kasashen waje dubu 14 da suke kasar Afganistan. Tun shekara ta 2001 ne sojojin Amurka suka mamaye kasar Afganistan bayan kifar da gwamnatin Taliban, amma kuma tun lokacin ne tashe tashen hankula suka kara yawa a kasar.