Carles Puigdemont Ya Shelanta 'Yancin Yankin Catalonia daga Kasar spain
A jawabin da ya gabatar dazun nan, Carles Puigdemont ya ce girmama kuri'ar raba gardama ne da aka kada ya shelanta 'yancin yankin na Catalonia.
Tun da fari dai tarayyar Turai ta yi gargadi akan ballewar yankin Catalonia daga Kasar Spain.
Shugaban majalisar tarayyar turai Donald Tusk ya bukaci shugabannin yankin na Catalonia da su kaucewa daukar matakin ballewa maimakon haka su bude tattaunawa da Madrid.
Donald Tusk ya bayyana haka ne sa'oi kadan gabanin bayanin da shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya yi wa Majalisar yankin a dazun nan.
Shugaban na majalisar turai ya bukaci ganin bangarorin Catalonia da Spain sun zauna kan teburin tattaunawa domin warware sabaninsu.
Ita ma gwamnatin kasar Spain ta gargadi shugaban yankin na Catalonia da akan duk wani yunkuri na ballewa daga Spain.
A daidai lokacin da Carles Puigdemont yake gabatar da jawabi a cikin majalisar, 'yan sandan Spain sun zagaye ginin da ke birnin Barcelona.
Kasashen tarayyar turai suna cikin zullumin abinda zai kai ya komo dangane da makomar yankin na Catalonia bayan ficewar Birtaniya daga cikin tarayyar.