Babban Sakataren Kungiyar "NATO" Ya Bukaci Da A Taimakawa Kasar Libya.
(last modified Sat, 14 Oct 2017 11:53:47 GMT )
Oct 14, 2017 11:53 UTC
  • Babban Sakataren Kungiyar

Babban Sakataren Kungiyar ta "Nato" Jens Stoltenberg ya fadawa jaridar kasar Italiya ta Onir, cewa;Wajibi ne kungiyoyin kasa da kasa da su taimakwa kasar Libya.

Jens Stoltenberg ya ci gaba da cewa manufa ita ce karfafa cibiyoyin da ake da su a yankunan da kuma basu horo ta fuskar tsaro.

Dangane da matsalar masu son yin hijira daga kasashen arewacin Afirka da ke kudancin tekun mediterrania , ya bukaci nahiyar turai da taimakwa, inda ya ce; Babu adalci da a bar kasashen Italiya, Girka, Spain da Portugal da wadannan matsala su kadai.

Kasar Libya tana daga cikin hanyoyin da masu son yin hijira suke bi domin shiga cikin turai.