Gwamnatin Rasha Ta Rufe Wasu Manyan Cibiyoyin Kasar Saboda Barazanar Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25027-gwamnatin_rasha_ta_rufe_wasu_manyan_cibiyoyin_kasar_saboda_barazanar_ta'addanci
Barazanar kaddamar da hare-haren ta'addanci a manyan cibiyoyin Rasha guda shida ciki har da tashoshin jiragen kasa da suke birnin Moscow ta tilasta wa jami'an kasar rufe cibiyoyin da nufin kare bullar hasarar rayukan jama'a.
(last modified 2018-08-22T07:00:51+00:00 )
Oct 18, 2017 15:32 UTC
  • Gwamnatin Rasha Ta Rufe Wasu Manyan Cibiyoyin Kasar Saboda Barazanar Ta'addanci

Barazanar kaddamar da hare-haren ta'addanci a manyan cibiyoyin Rasha guda shida ciki har da tashoshin jiragen kasa da suke birnin Moscow ta tilasta wa jami'an kasar rufe cibiyoyin da nufin kare bullar hasarar rayukan jama'a.

Tashar talabijin na biyu mallakin gwamnatin Rasha ta sanar da cewa: Gwamnatin Rasha ta dauki matakin rufe tashoshin jiragen kasa guda uku da suke birnin Moscow fadar mulkin kasar bayan barazanar kaddamar da hare-haren ta'addanci a tashoshin da aka samu ta hanyar wayar tarho daga wani mutum da ba a san ko wane ne ba.

Har ila yau barazanar kaddamar da hare-haren ta'addancin a filayen jiragen saman kasar ta Rasha guda biyu da suke kudu da kuma arewacin birnin Moscow, haka nan wani babban dakin karatu da ke birnin sun tilasta wa mahukuntan kasar rufe su tare da hana jama'a kusantarsu domin kare bullar hasarar rayuwa.

A halin yanzu haka dai jami'an tsaron Rasha suna ci gaba da yin amfani da na'urorin binciken bama-bamai gami da karnuka da nufin tabbatar da amincin cibiyoyin shida, tare da kokarin gano kafar da take yada irin wadannan barazana.