Jamus : Jami'an Tsaron Gabar Ruwa Sun Ceto Bakin Haure 615
https://parstoday.ir/ha/news/world-i2503-jamus_jami'an_tsaron_gabar_ruwa_sun_ceto_bakin_haure_615
Jami'an Tsaro gabar ruwa a Jamus sun sanar a wannan Laraba cewa sun ceto bakin haure 615 dake kokarin tsallaka tekun mediterranean.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 16, 2016 08:52 UTC
  • Jamus : Jami'an Tsaron Gabar Ruwa Sun Ceto Bakin Haure 615

Jami'an Tsaro gabar ruwa a Jamus sun sanar a wannan Laraba cewa sun ceto bakin haure 615 dake kokarin tsallaka tekun mediterranean.

Dama kafin hakan masu gadin gabar ruwan Italiya sun sanar da cewa adadin bakin haure da aka ceto a wannan Talata ya kai 951.

A cewar babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD bakin haure 9,495 ne suka isa Italiya ta teku tun daga farkon wannan shekara.

Bayanai sun nuna cewa kyakkyawan yanayi a yanzu a tekun na mediteranean ya taimaka sosai wajen samun yawaitar bakin hauren dake shigowa ta Libya.