G7 Da Kamfanonin Internet Sun Yunkuri Anniyar Toshe Farfaganda Ta'addanci
Gungun kasashe G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da mayan kamfanonin internet sun cimma matsaya kan toshe duk wata farfaganda dake da alaka da yada ta'addanci.
Bangarorin sun bayyana hakan ne a yayin wani taron ministocin harkokin waje na kasashen a Italiya.
Da yake bayyani kan matakin ministan harkokin wajen kasar Italiya, Marco Minniti, ya ce murkushe kungiyar 'yan ta'addan ta Da'esh a cibiyarta Raqqa a kasar Siriya babban koma baya ne a fagen daga ga kungiyar, amman hakan ba ya nufin babu kungiyar kwata-kwata ba.
Wannan dai shi ne karon farko da kasashen na G7 da wakilan mayan kamfanonin intarnet suka hadu kan teburin tattaunawa kan hanyoyin toshe yada ta'addanci a internet da sauren hanyoyin sadarwa na zamani.
Bangarorin dai sun bayyana cewa hanyoyin sadarwa na internet sun taimaka sosai wajen dauka, bada horo ga adadi mai yawa na mayakan ketare a kungiyar IS.