G7 Da Kamfanonin Internet Sun Yunkuri Anniyar Toshe Farfaganda Ta'addanci
(last modified Sat, 21 Oct 2017 05:34:18 GMT )
Oct 21, 2017 05:34 UTC
  • G7 Da Kamfanonin Internet Sun Yunkuri Anniyar Toshe Farfaganda Ta'addanci

Gungun kasashe G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da mayan kamfanonin internet sun cimma matsaya kan toshe duk wata farfaganda dake da alaka da yada ta'addanci.

Bangarorin sun bayyana hakan ne a yayin wani taron ministocin harkokin waje na kasashen a Italiya.

Da yake bayyani kan matakin ministan harkokin wajen kasar Italiya, Marco Minniti, ya ce murkushe kungiyar 'yan ta'addan ta Da'esh a cibiyarta Raqqa a kasar Siriya babban koma baya ne a fagen daga ga kungiyar, amman hakan ba ya nufin babu kungiyar kwata-kwata ba.

Wannan dai shi ne karon farko da kasashen na G7 da wakilan mayan kamfanonin intarnet suka hadu kan teburin tattaunawa kan hanyoyin toshe yada ta'addanci a internet da sauren hanyoyin sadarwa na zamani. 

Bangarorin dai sun bayyana cewa hanyoyin sadarwa na internet sun taimaka sosai wajen dauka, bada horo ga adadi mai yawa na mayakan ketare a kungiyar IS.