Switzerland: An Bude Taron Bada Tallafi Ga 'Yan Rohingya
(last modified Mon, 23 Oct 2017 11:00:25 GMT )
Oct 23, 2017 11:00 UTC
  • Switzerland: An Bude Taron Bada Tallafi Ga 'Yan Rohingya

A birnin Geneva na kasar Switzerland an bude wani taron muhawara na kasa da daka domin samar da tallafi ga 'yan gudun hijira Rohingya dake gujewa kisan kiyashin da ake musu a kasar Myanmar.

Taron wanda MDD da kungiyar tarayya Turai da Kowait suka shirya, na fatan tattara kudade da yawan su ya kai Dalar Amurka Miliyan 434 kafin nan da watan Fabrairu na shekara mai zuwa ta 2018.

Kawo yanzu dai taron ya samu alkawari da tallafin kudi da tuni aka zuba su da ya kai Dala Miliyan 100.

Tallafin dai zai shafi mutane miliyan 1,2 dake zube a lardin Cox's Bazar dake kudancin Bangaladesh, da wasu mazauna yankin su 300,000 sai kuma sabbi da tsofafin 'yan gudun hijira Rohingya kimanin 900,000.