Kasar Rasha Ta Yi Gwajin Sabbin Makamai Masu Linzami
Oct 27, 2017 02:57 UTC
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar a jiya alhamis cewa ta gwada wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango.
Sanarwar ta ce makamin mai suna "Topol-M" ana iya harba shi daga wata nahiya zuwa wata, kuma an gwada shi ne a cibiyar Plessetek da ke arewa maso yammacin kasar ta Rasha.
Bugu da kari Rashan, ta sanar da yin gwajin wasu makamai na ruwa a tekun Barents.
A can kasar Kazkystan ma jiragen yakin Rasha samfuron Tupolev-160 da Tupelov-95MC sun gwada wasu makaman tsibirin Kamtchtka.
Bayanin da ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta fitar ya ci gaba da cewa; Kasar tana akan ganiyar karfafa sojojinta ne da kuma bada horon kwarewa akan makaman Nukiliya.
Tags