Spaniya : Rajoy Ya Nemi A Tsige Shugaban 'Yan A Ware
Oct 27, 2017 09:46 UTC
Shugaban gwamnatin Spaniya, Mariano Rajoy, ya nemi majalisar dattijan kasar ta bada izinin tsige shugaban 'yan a ware na yankin Kataloniya.
Da yake wajabi yau Juma'a a gaban 'yan majalisar, Rajoy ya nemi a tsige shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont da mataimakinsa da mashawartan gwamnatin jihar.
Wannan dai na da manufar kalubalantar shirin gwamnatin ta Kataloniya na neman ballewa daga kasar ta Spaniya.
Haka kuma a cewar Mista Rajoy babban abunda gwamnatin Madrid ta sa a gaba shi ne shirye zaben yankin na Kataloniya a cikin watanni shida masu zuwa.
Tags