Yankin Catalonia ya balle daga Spain
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25200-yankin_catalonia_ya_balle_daga_spain
Majalisar dokokin yankin Catalonia na Spaniya ta kada kuri'ar ballewa daga kasar baki daya domin kafa kasarsu.
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 27, 2017 18:57 UTC
  • Yankin Catalonia ya balle daga Spain

Majalisar dokokin yankin Catalonia na Spaniya ta kada kuri'ar ballewa daga kasar baki daya domin kafa kasarsu.

Matakin ya samu goyon bayan 'yan majalisa 70 daga cikin 80 yayin da 'yan adawa suka kauracewa zaman.

Tun da farko Fira Ministan Spaniya Mariano Rajoy ya shaida wa 'yan majalisar dattawa cewa ana bukatar kawar da kwarya-kwaryar 'yancin da yankin yake da shi domin dawo da "doka, tafarkin demokuradiyya da kuma zaman lafiya" a Catalonia.Wannan rikici ya barke ne lokacin da jama'ar yankin suka kada kuri'a mai cike da rudani a farkon watan nan, inda suka amince da kafa kasarsu mai cin gashin kanta.

Gwamnatin Catalonia ta ce daga cikin kashi 43 cikin dari na wadanda suka kada kuri'a a zaben raba gardamar, kashi 90 ne suka goyi bayan a balle,sai dai kotun tsarin mulki ta Spain ta yanke hukuncin cewa kuri'ar ta sabawa doka.

Jim kadan bayan kada kuri'ar amincewa da kafa kasar ta Catalonia, majalisar dattawan Spaniya ta amince da matakin da ya bai wa gwamnatin kasar damar kwace iko da mulkin Catalonia.

Da yake daukar alkawarin dawo da doka da oda a Catalonia, Mista Rajoy, ya ce "sama da shekara 40 Spaniya ta kasance babbar kasa mai fada aji ta fuskar tattalin arziki,  don haka Catalonia ba za ta karya wannan tarihi ba".