Spaniya : Gwamnatin Madrid Ta Karbe Jagorancin Kataloniya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i25208-spaniya_gwamnatin_madrid_ta_karbe_jagorancin_kataloniya
Gwamnatin Madrid ta rushe jagorancin yankin Kataloniya jim kadan bayan da majalisar dokokin kasar ta amince ma gwamnatin da ta karbe ragamar jagorancin yankin Cataloniya.
(last modified 2018-08-22T11:30:54+00:00 )
Oct 28, 2017 06:30 UTC
  • Spaniya : Gwamnatin Madrid Ta Karbe Jagorancin Kataloniya

Gwamnatin Madrid ta rushe jagorancin yankin Kataloniya jim kadan bayan da majalisar dokokin kasar ta amince ma gwamnatin da ta karbe ragamar jagorancin yankin Cataloniya.

Firayi ministan na Spaniya, Mariano Rajoy, ya sanar a wani taron gaggawa cewa an yi hakan ne don dawo da doka a yankin na Kataloniya. 

Ko baya ga rushe jagorancin na Kataloniya, gwamnatin ta Madrid ta rushe majalisar yankin, domin shirya zabe a ranar  21 ga watan Disamba.

A jiya ne dai majalisar dokokin yankin na Kataloniya ta kada kuri'ar ballewa daga kasar ta Spaniya.

Dubun-dubatan masu rajin ballewar yankin ne dai suka taru a kusa da majalisar dokokin Kataloniya suna murna tare da rera taken yankin, jim kadan bayan da majalisar ta zabi ficewa daga kasar ta Spaniya.