Unicef : Tamowa Na Ci Gaba Da Gallazawa Yaran Rohingya
(last modified Fri, 03 Nov 2017 16:19:37 GMT )
Nov 03, 2017 16:19 UTC
  • Unicef : Tamowa Na Ci Gaba Da Gallazawa Yaran Rohingya

Asusun kula da yara na MDD wato Unicef ya fitar da wani sabon rahoto dace cewa alkaluman yara 'yan Rohingya dake fadawa cikin matsananciyyar tamowa dake kake yin kisa na dada karuwa.

A rahoton da ya fitar yau Juma'a Asusun na Unicef ya ce adadin ya yi muni sosai a wajen yara 'yan Rohingya da sukayi gudun hijira zuwan kudancin kasar Bangaladash.

Unicef ta ce adaddin yaran dake fama da yunwa ya linka har sau biyu a 'yan watanni baya baya nan.

Rahoton ya ce kimanin 'yan gudun hijira Rohingya 900,000 ne ke rayuwa a cikin mayuyacin hali kuma mafi akasarinsu yara ne.

Kakakin asusun na Unicef, Christophe Boulierac, ya bayyana a wani taron manema labarai a birnin Geneve cewa lamarin na da matukar daukan hankali.

Asusun na Unicef ya ce tuni jami'ansa suka fara kula da wasu yara 2,000 wanda suke fama da matsananciyyar tamowa.