Amurka Zata Kara Dorawa Wasu Jami'an Gwamnatin Venezuela Takunkumi.
(last modified Fri, 10 Nov 2017 06:18:45 GMT )
Nov 10, 2017 06:18 UTC
  • Amurka Zata Kara Dorawa Wasu Jami'an Gwamnatin Venezuela Takunkumi.

Ma'aikatar Kudi na kasar Amurka ta bada labarin cewa gwamnatin kasar zata bayyana wani shiri na kara dorawa wasu karin manya-manyan jami'an gwamnatin kasar Venezuela takunkumai.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar ma'aikatar kudin na Amurka tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba zata bayyana karin suniyen manya manyan jami'an gwamnati kasar Venezuela wadanda zata dorawa takunkumai don take hakkin bil'adama da kuma cin hani da rashawa..

Labarin ya kara da cewa takunkuman a wannan karon zai shafi wasu daga cikin wakilan sabuwar majalisar dokokin kasar Venezuela da aka kafa.

Kasar Venezuela dai ta yi ta fama da tashe tashen hankula a cikin watannin da suka gabata. Jam'iyyun adawa masu samun goyon bayan Amurka sun yi kokarin ganin shugaban kasar ta Venezuela Nikola Madoros ya sauka daga kan kujerara shugabancin kasar. Kuma gwamnatin kasar ta zargi Amurka da kokarin kifar da shugaba Madoros a lokacin. Amma gwamnatin Amurka ta dage kan cewa gwamnatin kasar ta Venezuela mai ci ta na take hakkin mutanen kasarta a dirar mikiyan da jami'an tsaron kasar sukayi yiwa masu zanga zanga a kasar.