Spain: 'Yan gudun Hijira Daga Afirka 600 Sun Tsira Daga Mutuwa
Nov 19, 2017 06:47 UTC
Ma'aikatan agaji na kasar Spain ne suka sanar da ceto da 'yan gudun hijirar da suka fito daga nahiyar Afirka a gabar ruwan kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a halin da ake ciki ana ci gaba da aikin ceton mutanen daga halaka.
Tun a jiya asabar ne dai sanarwar ta ce 'yan gunun hijirar sun fito ne daga kasar Libya domin shiga cikin kasashen turai inda suka fuskanci halaka a yankin Mursiya da ke kudu masu gabacin kasar Spain.
A bisa kididdigar hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ( IOM) kusan mutane 160,000 ne suka bi ta hanyoyi masu hatsari domin yin hijira zuwa Afirka a wannan shekara, kuma kusan 3000 daga cikinsu sun mutu.
Tags