Ruhani: Al'ummomin Yankin Nan Suna Murnar A Raunana Tushen Ta'addanci
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar al'ummomin yankin Gabas ta tsakiya suna cikin murnar nasarar da aka samu wajen raunana tushen ta'addanci a yankin yana mai bayyana bakin cikinsa dangane da yadda wasu kasashen yankin suke ci gaba da kokarin kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila.
Shugaba Ruhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron kasa da kasa kan Makon Hadin Kan Musulmi da aka bude a yau din nan a nan Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce a halin yanzu al'ummomin kasashen Iraki, Siriya, Labanon da ma sauransu suna cikin farin ciki saboda nasarar da aka samu wajen raunana tushen ta'addanci a yankin.
Shugaban na Iran ya kara da cewa a halin yanzu dai ana iya cewa wani sashi mai yawan gaske na makirce-makircen da manyan kasashen duniya ma'abota girman kai da kuma sahyoniyawa suka kulla wa al'ummomin yankin nan ya zamanto aiki baban giwa, kuma a nan gaba ma haka lamarin zai ci gaba da kasancewa.
Yayin da ya koma kan rigegeniya da wasu kasashen yankin Gabas ta tsakiya suke yi wajen kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila, shugaba Ruhani ya bayyana cewar lalle babban abin ciki ne yadda wasu kasashen a fili ma suke bayyanar da alaka da kuma abokantakarsu ga haramtacciyar kasar Isra'ila.
A yau ne dai aka bude taron kasa da kasa na hadin kan al'ummar musulmi da za a dau kwanaki uku ana yinsa.