Birtaniya : Boris Johnson Zai Fara Ziyara A Iran
(last modified Sat, 09 Dec 2017 05:54:50 GMT )
Dec 09, 2017 05:54 UTC
  • Birtaniya : Boris Johnson Zai Fara Ziyara A Iran

A wani lokaci a yau Asabar ne, ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Birtaniya, Boris Johnson, zai fara wata ziyara a Iran.

A yayin ziyarar wacce ita ce irinta ta farko, Mista Johnson, zai gana da takwaransa na Iran Muhammad Jawad Zarif, inda zasu tattauna batutuwa da suka shafi yankin ciki har da lalubo hanyoyin magance rikicin kasar Yemen da kuma yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya suka cimmawa da Iran.

Wata sanarwa da Boris ya fitar ta ce zai kuma tabo batun matar nan yar asalin kasashen Birtaniya da Iran, Nazanin Zaghari-Ratcliffe da ake tsare da ita a Iran.

Kafin ya fara ziyara a Iran ministan harkokin wajen kasar ta Birtaniya, Borins Johnson ya kai ziyara a kasar Oman, daya daga cikin kasashen dake shiga tsakani a wani sabani na tsakanin Iran da wasu kasashen yankin da kuma na yamma.