Rasha Ta Dauke Ofishin Jakadancinta Daga Kasar Yemen Zuwa Saudiyya
Dec 12, 2017 15:24 UTC
A yau talata ne kasar Rashan ta sanar da dauke ofishin jakadancinta daga birnin San'aa na kasar Yemen zuwa Riyahd na kasar Saudiyya.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha wacce ta fitar da sanarwar, ta kuma ci gaba da cewa; An rufe ayyukan ofishin jakadancin Rasha da ke Yemen na wani lokaci, kuma dukkanin ma'aikatan sun fice daga kasar ta Yemen.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova, ta ci gaba da cewa; Rufe ofishin jakadancin ya biyo bayan yadda al'amurra suke ci gaba da gurbata ne a cikin kasar ta Yemen.
Zakhrova ta kara da cewa; jakadan kasar Rasha a Yemen da dukkanin ma'aikatan diplomasiyya sun maida aikinsu zuwa birnin Riyahd.
Tags