Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Alkawarin Taimakawa Musulmin Rohinga
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta ce Kungiyar EU za ta taimakawa musulmin Rohinga na kasar Myanmar da suke gudun hijra a Bangladesh
Kamfanin dillancin labaran kasar Jamus ya nakalto Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini a birnin Strasbourg na cewa a kwai bukatar kudi da taimako na gaskiya domin taimakawa musulmin Rohinga da suke gudun hijra su koma kasar su da gaggauwa.
Mogherini ta ce kungiyar tarayyar Turai za ta taimaka daidai iyawarta ga wadanda suke son komawa gida daga cikin al'ummar musulmin Rohinga dake hijra a Bangladesh su koma kasarsu.
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta kara da cewa kungiyoyin bayar da agajin gaggauwa dake jihar Rakhine sun tabbatar da cewa suna iya karbar mutane har dubu dari biyar cikin musulmin Rohingar da suke yi hijra a Bangladesh.
Tun a shekarar 2012 ne dai musulmin Rohinga su ke fuskantar kisa da azabtarwa da kona gidajensu da dukiyarsu a hannun sojoji da yansanda da kuma masu tsattsauran ra'ayin addinin Buddha, irin wannan cin mutunci ya sake tasowa a karshen watan Augusta na shekarar 2017 da muke ciki.