Faransa : Macron Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Batun Siriya
(last modified Mon, 18 Dec 2017 11:03:28 GMT )
Dec 18, 2017 11:03 UTC
  • Faransa : Macron Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Batun Siriya

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya fada cewa wajibi ne ya tattauna tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya domin kawo karshen yakin basasar kasar, da kuma shirya hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na France 2 na kasar, shugaba Macron ya ce, ya canza matsayarsa game da abin da ya faru a baya, a baya sun yanke shawarar ba za su sake tattaunawa da al-Assad ba.

Ya ce za su yi nasara a yakin da suke yi da kungiyar IS a Syria nan da karshen watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Rikicin Siriya wanda aka shafe kusan shekaru takwas ana yinsa, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban daruruwan mutane, tare da tilasta wa wasu miliyoyin 'yan kasar yin gudun hijira.