An Kashe Yan Ta'adda 8 A Yankin Qafqas Na Kasar Rasha
Majiyar jami'an tsaro a kasar Rasha ta bada labarin kissan yan ta'adda 8 a yankin Qafqqas na kasar a wani fafatawa da suka yi da su a cikin kwanakin da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar jami'an tsaron kasar Rasha tana fada haka a yau Litinin kan cewa sun yi nasarar kashe wasu yan bindiga yayan wasu kungiyoyin yan ta'adda a yankin Qafqas a musayar wuta da suka yi da yan ta'addan a wurare biyu a yankin.
Labarin ya kara da cewa fafatawar ta auku ne a lardunan Dagistan da Karachay-Cherkessia na yankin Qafqas.Labarai bai bayyana lokacin da aka yi fafatawan ba.
Sojojin kasar Rasha dai suna aiwatar da wani shiri na musamman don yaki da ayyukan da'addanci a yankunan daban daban na kasar tun fiye da shekara guda da ta gabata.